Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- A yau Litinin ne matakin da Birtaniya ta dauka na haramtawa'yan Najeriya da wasu ƙasashen Afirka 10 shiga Birtaniya zai fara aiki saboda abin da gwamnatin Kasar ta ce tana yi na yaki da nau'in cutar korona Omicron da ta Bulla a wasu Kasashe da daman a duniya.
A bangare guda kuma Gwamnatin Najeriya Ta yi kira ga Birtaniya da ta janye matakin hana Yan Najeriya Shiga kasarta saboda nau'in korona Omicron.
Ministan Yada Labarai da Al'adu Lai Mohammed ne ya yi kiran yayin wani taron manema labarai a Abuja yau Litinin, yana mai cewa "babu hikima a wannan matakin".
342/